Sports
Kasuwar ‘yan kwallo Makomar Saka, Botman, Laporte, Kessie, Dembele
Liverpool ta bayyana sha’awarta ta dauko Bukayo Saka, dan wasan gefe mai shekara 20 daga Arsenal. Kwantiraginsa a Emirates za ta ƙare a 2024. (Transfer Window podcast, via Express)
Liverpool ta yi tayin ɗauko Franck Kessie, dan wasan tsakiya na AC Milan’s mai shekara 25 wanda tasa kwantiragin za ta ƙare a San Siro a karshen wannan kakar wasan. (Ansa – in Italian)
Barcelona wna son dauko Aymeric Laporte, dan wasan baya mai shekara 27 daga Manchester City a kakar wasa mai zuwa. (Sun)
Newcastle ana bukatar Sven Botman dan wasan baya mai shekara 21 na kungiyar Lille kan fam miliyan 30m a watan Janairu mai shigowa. (Mail)
Ousmane Dembele na iya komawa Newcastle bayan da kungiyar ta shirya tsaf domin raba dan wasan gefen mai shekara 24 da Barcelona. (Rudy Galetti on Twitter)
Arsenal na son raba Real Sociedad da dan wasanta Alexander Isak mai shekara 22, baya ga dan wasan Lille Jonathan David mai shekara 21. (The Athletic – subscription required)
Chelsea kuwa ta kusa raba Aurelien Tchouameni dan wasan tsakiya mai shekara 21 da kungiyarsa ta Monaco domin zai fi sauki kan dauko Declan Rice mai shekara 22 daga West Ham. (Daily Telegraph’s Matt Law on the London is Blue podcast, via Chelsea Chronicle)