Sports
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Alvarez, Coutinho, Trippier, Rudiger, Traore
Tottenham za ta dauko Philippe Coutinho mai shekara 27 daga Barcelona a kyauta, amma Barca ta fi son mika shi ga Everton ko Arsenal domin za su biya ta fam miliyan 17. (El Nacional – in Catalan)
Manchester United a shirye ta ke ta biya fam miliyan 16.8 domin daukan dan wasan gaban River Plate Julian Alvarez a wannan watan na Janairu bayan da ta sha gaban Bayern Munich, Barcelona, Real Madrid da Inter Milan kan dan wasan mai shekara 21. (Sport – in Spanish)
Newcastle ta kusa amincewa da Atletico Madrid kan dan wasan bayanta Kieran Trippier mai shekara 31. (Athletic – subscription required)
Idan Chelsea na son ci gaba da rike dan wasanta na baya Antonio Rudiger mai shekara 28, sai ta biya shi albashin da ya zarce na wanda ta ke biyan dukkan ‘ya wasan kungiyar. (Football Insider)
Rudiger na son a biya shi fiye da fam miliyan 16 ladar rattaba hannu kawai domin kawo karshen kwantiraginsa da Chelsea a kan hanyarsa ta komawa Real Madrid. (ABC – in Spanish)
Tottenham na ci gaba da nuna sha’awa kan dan wasan gaba mai shekara 25 da ke bugawa Wolves da Sfaniya Adama Traore. (Fabrizio Romano via This is Futbol)