Opinion
TAMBAYOYI 10 DA SHUGABA BUHARI ZAI AMSA DA KANSA
By Muhammad zahraddin
Tabbas idan kaji korafi akwai rashin gamsuwa kamar yadda indai kaji tambaya akwai abinda ya shigewa mutum duhu.
Assalamu Alaika Ya Shugaba Muhammad Buhari. Shugaban Najeriya.
Duba da ya yanayin yadda lamarin tsaro da sauran harkokin rayuwa, Wadan da sai da rai da lafiya ake batunsu suka kara tabarbarewa a Najeriya, Musamman Arewa, Yadda batun Ta’addanci da zullumin kai farmaki a garuruwa da hanyoyi, da wajajen noma ko wajajen neman halak (Kasuwanni) suka kara jefa rayuwar Takala cikin kunci, Sune dalilan rubuta wannan Wasika “Kai-Tsaye” cikin girmamawa gare ka.
Abinda yasa wannan wasika ta zama “Kai-Tsaye” kuma da sigar tambaya gare Ka ya Shugaban Najeriya Muhamnadu Buhari shine, Mu dai a Muslinci munkwana da sanin cewa akwai abinda aka yadda wani zai iyayi a madadin wani, Yayin da wani lamarin kuma kowa sai dai yayiwa kansa, Ma’ana wani baya wakiltar wani.
Haka kuma, Su kansu a abubuwan da ake iya bada wakilcin matukar akwai abinda ya shiga duhu tsakanin wanda aka aikawa wakilin da kuma wakilin, akwai damar tafiya kai tsaye zuwa ga wanda ya bada wakilcin, wannan shine dalilin neman wannan amsar daga gare ka Shugaban mu, Muhammadu Buhari domin kaine wanda Al’umar Najeriya muka dankawa Amanar jagorancin mu.
Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kasan cewa dukkannin Dan Adam Gajiyayye ne kuma Ajizine, Yakan dada himma ko ya rage a Al’amuran rayuwa, Hakan yasa Amsa wadannan (TAMBAYOYI GUDA 10) da kanka nake da yakinin ko ba komai wata hanyace da za kasan matsayin da Kake wanda mu kuma Yan’Najeriya muma zamu fa’idantu wajen ganin sauyi a zahiri yayin da Allah ya baka ikon amsawa kanka-da-kanka wadannan TAMBAYOYI wadanda basa bukatar wakilcin wani mukarrabin Ka.
Ga Tambayoyin daya-bayan-daya, wadanda Allah yasa ni ban yisu da kudurin izgili ko wata manufa ba, face na ganin Al’amuran kasa sun gyaru, wadan da kuma nake fatan zasu samu duba na tsanaki.
{1} Ya Shugaba Muhammadu Buhari, Anya kuwa Kana iya tuna yadda a baya kafin mu zabe ka, Ka dinga kushewa Shugabannin baya saboda abinda mu da Kai muka yadda sakaci ne wajen iya jagorancin Yan’Najeriya ?
{2} Anya kuwa Kana tuna yadda Ka dinga bibiyar Yan’Najeriya domin mu yarda zaka iya share mana hawaye har muka aminta muka baka Amanar kanmu data rayuka da dukiyoyin mu da hakkin kare mutuncin mu a 2015 ?
{3} Anya kuwa Kana iya tuna rahotannin yadda tsaffi masu shekaru da yawa (Old-ages) da Mata masu juna biyu (Pregnant women) da yadda wadansu daga cikin wadan da ke jinya a Gida dana Asbitoci suka rarrafa suka je suka wuni a layin zabe cikin ishurwa da yunwa da zafin rana domin zabar Ka ?
{4} Anya kuwa Kana iya tuna yadda Yan’Najeriya (Talakawa) suka ki ci, Suka ki sha, Suka dinga kankare kati domin aika maka da tallafin kudi domin Ka kai ga Nasara a zaben 2015 ?
{5} Anya kuwa Kana iya tuna yadda rashin lafiya wadda tana kan kowa ta same ka, Jin kadan bayan an zabe ka, Talakawan da suka zabe Ka suka kasa zaune suka kasa tsaye a gidajensu da makarantunsu da Masallatai da Majalisu dare da rana suka dinga yi maka addu’a domin ka samu lafiya ka futar dasu daga takaici ?
{6} Anya kuwa Shugaba Buhari a matsayin Ka na Musulmi kana iya tuna kalaman dake cikin rantsuwar kama mulki da ka saba lokutan rantsar dakai a Abuja da sauran jawaban da kayi a ranar ?
{7} Shin Shugaba Buhari Kama yarda cewa Najeriya da Yan’Najeriya musamman Talakan Arewa na cikin mawuyacin hali da zullimin tsaro ?
{8} Ya Shugaba Muhammadu Buhari shin Kasan cewa yin tallaki domin jajantawa da yin sannu hadi da addu’a ga wanda ke cikin damuwa koda bazai samu waraka ba abune mai dadi ga wanda ke cikin irin wannan hali? Kamar yadda sanda ka kwanta rashin lafiya a Landan Talakawan ka sukai tayi maka addu’a harda yin yanka da bada sadaqa, wanda nasan a lokacin inda ace Birnin Landan kamar nisan Jakara zuwa Gauron Dutse yake da duk da baza’a basu damar ganin ka ba, dasun yi dafifi a garin da kake jinya domin nuna Alhini amma Kai gashi gari ya gari, jirgi kawai zaka hawo ka jajantawa Katsinawa da Sokkwatawa da sauran gururuwan Arewa amma abin ya faskara.
{9} Har ila yau, Anya kuwa Buhari a matsayin Ka na Musulmi wanda ya samu tarbiyyar Kasar Hausa, Kayi makarantar addini kamar yadda duk Musulmi keyi, Ka yarda cewa akwai hisabi bayan mutuwa kuma cikin hisabin za’a tambayeka duk abinda kayi dama wanda yaki yi wanda a dalilin hakan rayuwar mutane da mutuncin su ke salwanta ?
{10} Shin sai a wanne lokacin ne Shugaba Buhari Kake zatan Alkawura da kuma kyawawan kudurori da ka zawarci kuri’un Yan’Najeriya sazu cika, In kuma kai kanka ya yanke haso, abin yafi karfin ka to yaushe zaka yiwa Yan’Najeriya bayani kai tsaye saboda musan mataki na gaba ?
Wadannan suke jerun Tambayoyi ko kuma ka lallesu a matsayin tuhumar da indai Allah ya baka iko ka iya amsawa Kanka-da-Kanka su kuma ka dauki matakin da ya dace yanzu-yanzu to kuwa nan take muma zamu ji amsar a jikin mu da kuma ganin amsar da idan mu, domin amsar Tambayoyin kamar yadda nace a aikace Yan’Najeriya zamu gani.
Allah ya baka ikon dubawa dana daukar matakin da ya dace akan lokaci.
Ko wanne Dan kasa da iyakacin aikin da hurumin kundun mulki ya sahale masa, wannan shine nawa hurumin a matsayin na na Dan Jarida mai fatan ganin Kasata, Najeriya ta kyautatu.