News
Ƴan Sanda sun kama miji bisa zargin kashe matar sa a Nassarawa
Daga kabiru basiru fulatan
Yan sanda a Jihar Nassarawa sun kama wani mutum mai suna Ovye Yakubu bisa zargin hallaka mai ɗakin sa, Esther Aya a gidan su da ke unguwar Sabonpegi-Shamu a garin lafia.
Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta jihar, Ramhan Nansel ne ya baiyana haka a tattaunawa da Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Asabar a Lafia.
Nansel ya ce an cafke wanda a ke zargin ne a juya Juma’a bayan da Rundunar ta samu rahoton kisan sakamakon ƴar rigima da ta shiga tsakanin su a jiyan.
Ya ce tuni dai a ka faɗaɗa bincike a kan wanda a ke zargin bayan da a ka kai shi sashen binciken sirri na rundunar, domin gano musabbabin kisan.
Ya ce tuni a ka kai gawar marigayiyar mutuware domin bincike.
Sai dai kuma NAN ta jiyo cewa mijin ya kashe matar ne sakamakon cacar-baki da ta ɓarke a tsakanin su.