Sports
Makomar Milinkovic-Savic, Haaland, Bissouma, Sanchez, Pogba
Daga kabiru basiru fulatan
Manchester United na ƙoƙarin ɗauko Sergej Milinkovic ɗan wasan tsakiya ɗan ƙasar Serbia mai shekara 26 daga Lazio. (Calciomercato – in Italian)
United ta kuma yi wa Paul Pogba, ɗan wasanta na tsakiya mai shekara 28 tayin fam 500,000 a kowane mako idan ya amince ya ci gaba da buga tamaula a ƙungiyar. (Sun)
Sai dai Pogba ya musanta cewa United ta yi ma sa wannan tayin mai matukar tsoka. (Mail)
Liverpool na shirye domin yi wa dan wasan Sfaniya da Barcelona Gavi mai shekara 17 tayin fam 80,000 a kowane mako idan ya amince ya koma Anfield. (El Nacional – via Mail)
Inter Milan ta yi wa Everton tayin Alexis Sanchez kyauta. Kwantiragin tsohon dan wasan na Arsenal da Manchester United mai shekara 33 ta kare a Milan. (Sun)
Aston Villa na sha’awar Yves Bissouma, dan wasan tsakiya na Brighton da Mali mai shekara 25. (Sky Sports)
Liverpool ta ki amincewa da tayin fam miliyan 7 da Watford ta yi ma ta kan Nathaniel Phillips, dan wasanta na baya mai shekara 24. (Football Insider)
Liverpool kuma ba za ta amince da dan wasanta na gaba Divock Origi mai shekara 26 ya koma wata kungiyar ba a wannan watan na Janairu. ((Liverpool Echo)
Ainsley maitland Niles mai shekara 24 na kungiyar Arsenal da Ingila ya isa Italiya domin kammala sauya sheƙar da zai yi zuwa AS Roma ta Gasar Serie A. (football.london)
Tsohon mai ƙungiyar Newcastle Mike Ashley na duba yiwuwar saye ƙungiyar Derby County ta Ingila wadda ke matakin Division 1. (Telegraph)
Barcelona kuwa ita ce ta bayan nan da ke nuna sha’awar ɗaukan Antonio Rudiger, dan wasan bayan na Chelsea mai shekara 28 da zarar kwantiraginsa ta ƙare a ƙarshen wannan kakar wasan. (Sky Sports)
Lionel Messi dan wasan Paris St-Germain mai shekara 34 na son barin ƙungiyar bayan kakar wasa ɗaya kawai idan ta gaza lashe Gasar Zakarun Turai a bana. (El Chiringuito TV, via Mirror)