News
Sojoji sun hallaka ƴan ta’adda 5 yayin da ƴan ISWAP ke yunƙurin shiga Biu
Daga kabiru basiru fulatan
Sojoji sun hallaka ƴan ta’adda 5 yayin da ƴan ISWAP ke yunƙurin shiga Biu
Rundunar Sojin Ƙasa ta ‘Operation Hadin Kai’ ta ce ta lallasa ƴan Boko Haram da ISWAP.
Sojojin sun lallasa ƴan ta’addan ne yayin da su ke yunƙurin kurdawa cikin garin Biu a Jihar Borno.
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojin Ƙasa, Onyema Nwachukwu shine ya baiyana haka a wata sanarwa a yau Lahadi.
Ya ce sojojin runduna ta 231 da 331, ƙarƙashin sashe na 2 ne su ka fatattaka yan ta’addan.
Ya ce ƴan ta’addan sun gamu da gamon su ne yayin da sojoji su ka dirar musu sanda su ke yunƙurin shiga garin Biu ta ƙauyen Maina Hari village in Biu a jiya Asabar.
Ya ce sojojin sun gwada kwanjin su a kan ƴan ta’addan har su ka hallaka 5 da ga cikin su, in da su ka fatattaki sauran.
Ya ce kuma sojojin sun kwace kayan yaƙi iri-iri a hannun ƴan ta’addan.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
