News
Ɗumbin aiyukan El-Rufai za su sa na ɓata a Kaduna — Buhari
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis ya yabawa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai bisa ɗumbin aiyukan ci gaba da ya yi ya canja yanayin jihar.
Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da filin Murtala Mohammed Square da a ka yi wa kwaskwarima da kuma Gadar Sama ta Kawo, Buhari ya ce aiyukan ci gaba da El-Rufai ya yi ya burge shi.
Ya ce ɗumbin aiyukan da El-Rufai ya yi na canja yanayin Kaduna abin yabawa ne, in da ya ce ko shi ma mazaunin jihar sai ya yi da gaske zai iya yawo a garin.
“Na dade ina zaune a Kaduna tsawon lokaci amma yanzu sai na ɓata a garin nan. Ka canja Kaduna sosai. Ka rubuta tarihin ka da haruffan gwal,” in ji Buhari yayin da ya ke ƙaddamar da aikin Murtala Mohammed Square.
Buhari ya yabawa El-Rufai a bisa kokarin da ya yi a jihar sa, inda ya ce mutane a faɗin ƙasar nan na yaba masa a bisa ɗumbin aiyukan da ya yi.
A nashi jawabin, El-Rufai ya ce Gwamnatin Taraiya ce ta fara gina Murtala Muhammed Square tun a 1970 sannan ta danƙa ta a hannun gwamnatin Kaduna.
“Murtala Mohammed Square ta sha kwaskwarima inda yanzu ta zama filin da za a riƙa yin kasuwanci iri-iri da kuma filayen wasanni kamar su kwallon kafa da sauran su,” in ji shi.
Kafin nan, Shuagaban Ƙasar, wanda ya ke Kaduna domin ziyarar aiki ta kwanaki 2, ya ƙaddamar da aiyuka a Kafanchan kuma gobe juma’a zai je Zariya ya ƙaddamar da wasu aiyukan.