News
Buhari zai samar da ingantantaccen tsaro sama da yadda ya ke kafin ya hau mulki — Minista
Daga yasir sani abdullahi
Ministan Harkokin Ƴan Sanda, Maigari Dingyadi ya ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na fafutukar gyara harkar tsaro ya kuma inganta ta samma da yadda ta ke lokacin da ya hau mulki.
Dingyadi ya baiyana haka ne a yayin ƙaddamar da Kwamitin Wayar da kai da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe na Yan Sanda, PPCC, na Arewa-Maso-Yamma a ranar Alhamis a Sokoto.
Ya ce ƙaddamar da kwamitin wani yunƙuri ne Gwamnatin Taraiya wajen ƙara inganta aiyukan ƴan sanda domin ƙarfafa aikin su bisa kan doka da kuma kare haƙƙin ɗan adam.
Ya yi nuni da cewa PPCC wani tsari ne da a ka ƙirkiro domin magance matsalar rashin jituwa tsakanin ƴan sanda da al’umma a yayin gudanar da aikin su.
Dingyadi ya ƙara da cewa kwamitin zai baiwa al’umma damar kai ƙarar cin zarafi da ga ƴan sanda domin ɗaukar mataki da kuma daƙile ta’adar.
“Hakan na cikin ƙudurin shugaban ƙasa na samun ingantantaccen tsaro da ci gaban ƙasa,” In ji Ministan.
Ya kuma tabbatar da ƙudurin Buhari na inganta harkokin tsaro domin samar da ƙasa mai cike da zaman lafiya da tsaro sama da yadda ya samu ƙasar a 2015.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News5 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
