Babban wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar mai shekara biyar a Kano, Abdulmalik Tanko, ya faɗa wa kotu cewa ba shi da lauya sannan ya buƙaci gwamnatin jihar ta sama masa lauyan.
“Ba mu da lauya a yanzu saboda ba ma iya magana da kowa, amma ina roƙon gwamnati ta ba mu lauya,” in ji Abdulmalik a zaman kotun na yau Litinin.
Su ma sauran mutum biyun; Fatima da Hashin Isiyaku, sun amince da abin da Abdulmalik ya faɗa na neman lauyan.
Lauyan gwamnati Musa Lawal ya ce gwamnatin za ta ba su lauyan kamar yadda suka buƙata. Da ma dai haka doka ta tanada saboda laifin da ake zargin su da aikatawa mai girma ne.
Mai Shari’a Sulaiman Na Abba ya ɗaga zaman shari’ar zuwa 14 ga watan Fabarairun 2022 da ƙarfe 2:00 na rana.
A watan da ya gabata ne ‘yan sanda suka kama mutum uku da ake zargi da sacewa da kuma kashe ‘yar shekara biyar ɗin a unguwar Dakata Kawaji da ke birnin Kano.