Connect with us

Sports

Kasuwar yan ƙwallo: Makomar Mbappe, Rice, Sule, Benzema, Traore, Raphinha

Published

on

FB IMG 16427424287468398
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

Ana alakanta ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe da komawa Real Madrid idan kwantiraginsa ya ƙare da Paris St-Germain a karshen kaka, sai dai ɗan wasan mai shekara 23 ya ce bai yanke hukunci ba kan makomarsa. (Amazon Prime, via Mirror)

Kocin West Ham David Moyes ya ce Declan Rice mai shekara 23 ya haura £100m, yayinda ƙungiyoyi irinsuManchester United, Chelsea da Manchester City ke zawarcinsa. (Metro)

Advertisement

Chelsea ta fuskanci babban koma baya bayan ɗan wasan da take hari Niklas Sule, mai shekara 26, ya amince ya koma Borussia Dortmund daga Bayern Munich. (Mirror)

Arsenal ita ma ta fuskancin babban koma baya a kokarin farautar ɗan wasan nan Christopher Nkunku mai shekara 24 bayan RB Leipzig ta dage cewa ɗan wasan zai tsawaita zama da ita. (Sky Sport Germany – in German)

Ɗan wasan Faransa Karim Benzema ya buƙaci tattaunawa da shugaban Real Madrid Florentino Perez yayinda ya ke fargabar rasa gurbinsa a ƙungiyar idan aka sayo Erling Braut Haaland daga Borussia Dortmund(Onze – in French)

Advertisement

Manchester United ta amince da cinikin £12m kan ɗan wasan tsakiya a Brazil Andreas Pereira, da Flamengota gabatar da tayi(Universo, via Sun)

James Garner na fatan ci gaba da zama a Manchester United yayinda wa’adin zaman aro da yake a Nottingham Forestya zo karshe(Manchester Evening News)

KocinWolves Bruno Lage ya goyi bayan kwantiragin £29m kan ɗan wasan Sifaniya Adama Traore zuwaBarcelona.(Mirror)

Advertisement

Lage na fatan kara karfafa kungiyarsa ta Wolves sa karshen kaka. (Birmingham Live)

Kocin Leeds United Marcelo Bielsa ya kare kungiyar kan ƙin sayen manyan ‘yan wasa a watan Janairu. (Mail)

Leeds United ta gaza sayar da Raphinha, mai shekara 25 a watan Janairu amma tana fatan farautar Kalvin Phillips da Illan Meslier a sabuwar kaka. (Athletic – subscription required)

Advertisement

Ɗan wasan Jamus Robin Gosens, ya ce yana tuna tayin da Newcastle United ta gabatar kan sa kafin ya koma Inter Milan daga Atalanta a watan Janairu. (Kicker – in German)

Everton da Leicester City na cikin ‘yan wasan Firimiya da ke farautar ɗan wasan Bristol City asalin Ingila Alex Scott. (Football Insider)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *