Connect with us

Sports

Najeriya ta fasa dauko koci dan kasar waje

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da sauya fasalin yadda tawagar kasar, Super Eagles za ta kasance.

Advertisement

NFF ta ce mai horad da kungiyar na riko Augustine Eguavoen zai ci gaba da aikin da yake kai, yayin da tsohon dan wasan Eagles din Emmanuel Amuneke zai zame masa mataimaki.

A sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun sakatare janar nata Dr Muhammad Sanusi ta ce ” hukumar kwallon kafar Najeriya ta kai karshen barin Augustine Eguavon ya ci gaba da horar da Super Eagles a matsayin kocin riko, yayin da Emmanuel Amuneke zai yi masa mataimaki.

Haka ma hukumar ta ce tsohon dan bayan kasar Joseph Yobo da kuma Salisu Yusuf za su shiga cikin mataimaka hudu da kungiyar ta nada.

Advertisement

Daman Amuneke ya yi aiki da NFF a matsayin kocin ‘yan-kasa da shekara 20.

Sanarwar ta kuma fito karara ta bayyana cewa ta dakatar da yarjejeniyar da ta tsara kullawa da Jose Peseiro, wanda aka sa ran cewa zai karbi aiki daga Eguavoen da zarar an kammala gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Emmanuel Amuneke ne ya ci wa Nigeria duka kwallaye biyun da ta ci kofin nahiyar Afrika a shekarar 1994 a karawarsu da Zambia.

Advertisement

Kazalika shi ne ya ci kwallon da ta bai wa Najeriya damar cin lambar zinare a gasar Olympics ta Atlanta 96 da aka yi a Amurka.

Tsohon dan kwallon ya kuma kai Tanzania gasar AFCON a 2019, haka nan mamba ne a kwamitin bincike da nazari na hukumar kwallon kafa ta duniya da ma CAF ta Afrika.

NFF ba ta fito ta bayyana dalilin fasa dauko mai horarwa ba daga kasashen waje, to amma ana ganin sauye-sauyen da ta bullo da su na da nasaba da kasa tabuka abin a-zo-a-gani da Super Eagles ta yi a gasar AFCON da aka kammala ranar Lahadi a Kamaru, wadda Senegal ta yi nasara cin kofin a wasan karshe da Masar.

Advertisement

A wata mai zuwa ne Najeriya za ta kara da Ghana gida da waje, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar cikin watan Nuwamba.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *