Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Kane, Mane, Xhaka, Tielemans, Kean, Vidal, Kelly
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Kyeftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ‘yana cikin farin ciki’ yayin da kocin Tottenham Antonio Conte da ƙungiyar ke son ɗan wasan mai shekara 28 ya ci gaba da zama da su, sai dai har yanzu bai yanke shawara kan makomarsa. (Fabrizio Romano, via Express)
Ɗan wasan gaba a Liverpool da Senegal Sadio Mane, mai shekara 29, mai yiwuwa ya bar ƙungiyar a wannan kaka idan ya samu tayi daga Real Madrid ko Barcelona. (Goal, in Spanish)
Roma babu mamaki ta yi kokarin sake miƙa tayinta kan ɗan wasan Arsenal asalin Switzerland mai buga tsakiya Granit Xhaka, ɗan shekara 29, a wannan kakar summer. (football.london)
Manchester United na harin ɗan wasan Leicester City asalin Belgium mai buga tsakiya, Youri Tielemans, ɗan shekara 24 kan £40m. (Star)
Da dama daga cikin manyan ƙungiyoyin firimiyar Ingila na harin ɗan wasan Reims Hugo Ekitike. Newcastle Uniteddai ta gaza kulla yarjejeniya da bafaranshen ɗan wasan mai shekara 19 a watan Janairu. (90 Min)
Paris St-Germain ta kwaɗaitu da ɗan wasan Italiya mai kai hari Moise Kean. Matashin mai shekara 21 na zaman aro yanzu haka a Juventus daga Everton kuma ƙungiyar ta Seria A na da zabin tabbatar da zamansa kan euro miliyan 28 (£23.6m). (Calciomercato, via Football Italia)
Newcastle United na shirin dauke dan wasan Bournemouth Lloyd Kelly, mai shekara 23, a wannan kaka ko da kuwa sun koma kasan teburi. (Football Insider)
Tottenham Hotspur na son cimma yarjejeniya da ɗan wasan Inter Milan asalin Chile mai buga tsakiya, Arturo Vidal, ɗan shekara 34. (La Latercera, in Spanish)
Norwich City da Rangers sun soma bayyana sha’awarsu kan ɗan wasan Schalke mai shekara 28 da ke tsaron raga Martin Fraisl, wanda kwantiraginsa ke karewa a wannan kakar.. (Mail)
Ɗan wasan Real Madrid da Croatia Luka Modric, mai shekara 36, ya ce zai ci gaba da murza leda har lokacin da zai cika shekara 40 a duniya. (Marca)
Mike Ashley har yanzu na son sayen ƙungiyar Derby County sai dai ya ce lokaci na kure ma sa. (Star)