Connect with us

Sports

Kasuwar ƴan ƙwallo Makomar Ronaldo, Rice, Mane, Kessie, Tielemans, Saka

Published

on

FB IMG 16445581673568046
Spread the love

Ɗan wasan gaba a Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 37 na son ayita ta kare tsakaninsa da wakilinsa kan makomarsa a Manchester United sakamakon yadda rayuwa ta yi masa tsananin tun bayan komawarsa Old Trafford. (Star)

Mai buga tsakiya a Ingila Declan Rice, da ƙungiyar Chelsea da Manchester United da City ke hari, ya jadada burinsa na lashe kambuna da wasanni a Champions League, sai dai kuma ɗan wasan mai shekara 23 ya tabbatarwa magoya-bayansa na West Ham cewa yana tare da su don haka kar su dakata jita-jita. (Standard)

Mai tsaron ragar Chelseada ake biya £72m Kepa Arrizabalaga, ɗan shekara 27, na iya bankwana da Stamford Bridge a wannan kakar. Babu dai alamar ƙungiyar za ta yi kokarin hana shi tafiya idan hakan shi ne zaɓinsa. (Sun)

Advertisement

Barcelona na samun nasara a cinikin ɗan wasan AC Milan da Ivory Coast Franck Kessie a wannan kakar. Matashin mai shekara 25 ya kasance wanda ita maLiverpoolke zawarci(Marca) 

Ɗan wasan Liverpool Sadio Mane, mai shekara 29, na da zaɓin barin ƙungiyar, kuma tuni Barcelona da Real Madrid suka kwaɗaitu da saye matashin ɗan kasar Senegal. (Goal, via Mirror)

Leicester City ta rage kuɗin da ta sanya kan ɗan wasa Youri Tielemans, mai shekara 24 daga £60m zuwa £35m wanda Arsenal da Manchester United ke rige-rigen saye shi a wannan kakar. (Het Nieuwsblad, via Metro)

Advertisement

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya amince da cewa akwai kalubale a iya samun nasara a gasar zakarun Turan bana yayinda ta gabartar da sabon kwantiragi kan ɗan wasanta mai shekara 20 Bukayo Saka – da ake alakantawa da Liverpool(Express)

Ɗan wasan da Manchester United ke hari Manuel Akanji na son a masa karin albashi a Borussia Dortmund(Bild, via The Sun)

Kocin Sifaniya mai shekara 51 Luis Enrique, ya kasance mutumin da Manchester United ke son bai wa aikin kociyanta. (Star)

Advertisement

Cesar Azpilicueta na Sifanya na son tattaunawa da Chelsea kan makomarsa, yayinda ake alaknata ɗan wasan mai shekara 32 da Barcelona idan kwantiraginsa ya kare a wannan kakar. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Barcelona na son sayen sabbin masu tsaron baya hakazalika ta shirya sayar da Sergino Dest mai shekara 21 saboda ta samun karin kudi a kokarin sayo ɗan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland, mai shekara 21. (ESPN)

Sabon kocinTottenham Fabio Paratici na son ya mayar da hankali kan sayo matasan ‘yan wasa da yanzu ake gano baiwarsu da wadanda kwantiraginsu ke cikin rashin tabbas, yana dai sanya ido kan ɗan wasan Faransa Mamadou Coulibaly mai shekara 21 wanda yanzu haka ke taka leda a Monaco.(Mail)

Advertisement

Robert Lewandowski na Bayern Munich na burin komawa Real Madrid. (AS – in Spanish)

Tsohon ɗan wasan Manchester United da Arsenal Alexis Sanchez, mai shekara 33, na gab da samun sabon kwantiragi daga Inter Milan, amma dole albashinsa ya ragu. (Gazzetta dello Sport – in Italian)

Arsenal ta kammala yarjejeniyar saye mai tsaron raga Matt Turner daga New England Revolution kan £7.5m(Mail)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *