News
Ganduje ya umarci jami’an tsaro su kamo waɗanda su ka kashe matar aure a Kano
Daga yasir sani abdullahi
Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta bincike da kamo waɗanda su ka kashe wata matar aure mai suna Rukayya Mustapha a cikin gidanta da ke unguwar Danbare, Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Kano.
Gwamnan ya bada umarnin ne jiya Litinin a lokacin da ya kai ziyarar jajae ga iyalan marigayiyar a unguwar Dorayi dake Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar.
Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna, Hassan Musa Fagge, Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya ce gwamnatinsa ta duƙufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.
” cikin tsananin kaɗuwa mu ka samu labarin rasuwar marigayiya Rukayya Mustapha. Ina mai tabbatar muku da cewa ba za mu bar wananan abun haka kawai ba, dole sai an nemo waɗanda su ka aikata wannan mummunan aiki”. Inji Ganduje
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ina Allah wadai da wannan aika-aika tare da addu’ar Allah ya jikan ta yasa tana Jannatul Firdaus tare da baiwa ‘yan uwanta hakurin jure rashin,” in ji Ganduje.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayyana cewa kawo yanzu an kama mutane 5 da ake zargi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin zaƙulo wadanda suka kashe matar.
Ya kuma yi nuni da cewa, wadanda su ke ta’ammali da miyagun kwayoyi ne ke aikata irin wadannan laifuffuka, shi ya sa suke kama duk wadanda suke yin safarar miyagun kwayoyi domin dakile sake afkuwar irin lamarin.
Dikko ya kuma bayar da tabbacin cewa, hukumomin tsaro za su ruɓanya kokarinsu na ganin ba a sake samun faruwar irin waɗannan laifuka ba nan gaba.
A tawagar gwamnatin a kwai ta Daraktan Hukumar Ƴan Sanda na Farin Kaya, DSS Alhassan Muhammed da sauran kwamishinoni na jihar.