News
Majalisar Dattijai ta amince da cin gashin kan ƙananan hukumomi, majalisun dokoki da ɓangaren Shari’a
Daga kabiru basiru fulatan
A yau Talata ne Majalisar Dattijai ta kaɗa ƙuri’ar yin gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 wanda ya baiwa majalisun jihohi, ɓangaren Shari’a ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu a fannin kudi.
A ƙuri’ar da aka kaɗa a zauren majalisar, ƴan majalisar dattawa 83 ne su ka kaɗa kuri’ar amincewa da cin gashin kan harkokin kuɗi ga majalisun dokoki da bangaren shari’a da ƙananan hukumomin, yayin da Sanata ɗaya ya ƙi amincewa da hakan.
Sanatoci 92 ne suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da ƙudirin yin gyaran fuska ga ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomin, yayin da Sanatoci biyu suka ki amincewa.
A hannu guda kuma, Majalisar ta yi watsi da shirin sauya sunan Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi da ke Jihar Filato zuwa Gwul.
A ƙuri’ar da aka kaɗa, ‘yan majalisar dattawa 67 ne su ka kaɗa ƙuri’ar neman sauya sunan, yayin da 28 suka ƙi amincewa.
Shawarar ta gaza cika kaso biyu bisa ukun da a ke bukata.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, kafin Amincewa da kowane kudiri , dole ne ya samu rinjaye na kashi biyu bisa uku a zauren majalisar dattawa.