News
Farashin ɗanyen mai ya ƙara tashi a duniya bayan ƙauracewa man Rasha

Daga idris Abubakar
Farashin ɗanyen mai ya ƙara tsada a ranar Laraba, yayin da ƴan kasuwa suka rungumi man da ba na Rasha ba, wanda zai haifar da tsadar man a Birtaniya.
Ɗanyen mai samfurin Brent – ma’aunin farashin mai a duniya – ya haura dala 113 a kowace ganga, cirawa mafi girma tun watan Yunin 2014.
Ƴan kasuwa na shan wahalar sayar da man Rasha, duk da sun sassauta farashi, saboda wahalar ɗauko man da kuma biyan kuɗi sakamakon rikicin Ukraine.
Farashin Gas ma ya lunka.
Kusan kashi 70 na ɗanyen man Rasha babu wanda zai saya, kamar yadda wani kamfanin makamashi na Energy Aspect na Birtaniya ya bayyana.
Ƴan kasuwa dai na tsoron kada su fuskanci fushin hukumomi sakamakon takunkumin da ƙasashen yammaci suka kakabawa Rasha.