News
Gobara ta ƙone kayaiyakin tallafi na N18.5m a hukumar SEMA ta Kano

Daga kabiru basiru fulatan
A jiya Juma’a ne gobara ta ƙone kayaiyyakin tallafi na Hukumar Jin-ƙai ta Jihar Kano, SEMA, wanda kumar su ta kai naira miliyan 18.5.
Gobarar ta kone rumbun ajiye kayan da ke Makarantar First Lady a unguwar Mariri, Ƙaramar Hukumar Kumbotso.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa ɗaukacin kayan da ginin sun ƙone ƙurmus.
Shugaban hukumar SEMA, Alhaji Saleh Jili, ya ce kayayyakin, da su ka haɗa da katifu 450, fulo 450, katan ɗin famfas 665 duk sun ƙone ƙurmus.
A cewar Jili, har su kekunan ɗinki, injin nika da sauran injina duk sun ƙone, inda ya ce kayan sun kai na Naira miliyan 18.5.
Jili ya ƙara da cewa kayayyakin irin wanda Gwamnatin Taraiya ta kawo wa jihar tallafi ne, inda ya dora musabbabin gobarar a kan ƙona ciyawa da ma’aikatan wajen ke yi.