Connect with us

News

Gwamnatin Legas na bincike kan waɗanda suka raba man fetur a wurin biki

Published

on

Screenshot 20220305 162239
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

Gwamnatin Jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ce tana bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta inda wasu ke raba man fetur a cikin jarakuna a matsayin kyautar halartar biki.

Kwamashinan Yaɗa Labarai na Legas, Gbenga Omotoso, ya ce “shakka babu wannan lamarin abin haɗari ne kuma zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi”.

A ‘yan awannin da suka gabata ne bidiyon ya ɓulla, inda aka ga jarakunan fetur masu lita 10 a jere da za a raba wa mahalarta bikin. Daily Trust ta ce Chidinma Pearl Ogbulu ce ta shirya taron don murnar naɗa ta a matsayin Erelu Okin.

Advertisement

Yanzu haka ‘yan Najeriya na fama da ƙarancin man fetur, inda suke shafe awanni masu yawa a kan dogayen layuka.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *