Connect with us

News

BBC, CNN da kafofin labaran Yamma sun dakatar da aiki a Rasha

Published

on

FB IMG 1646481788261
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Gidajen talabijin na CNN da ABC da CBS da ke Amurka sun ce sun dakatar da yaɗa shirye-shirye a rasha yayin da aka ƙaddamar da wata doka da za ta hukunta masu yaɗa labaran ƙarya, kamar kamfanin labarai na Rasha TASS ya ruwaito.

Advertisement

Tun farko BBC ta ce ta dakatar da aiki a cikin Rasha amma za ta ci gaba da aiki daga wajen ƙasar.

“CBS ta dakatar da watsa labarai daga Rasha yayin da muke ci gaba da duba abubuwan da ke faruwa ga tawagarmu da take can saboda sabuwar dokar da aka kafa a yau,” a cewar CBS.

Shi ma ABC ya ce “sakamakon sabuwar dokar tantancewa a Rasha a yau, wasu daga kafofin yaɗa labarai na Yamma ciki har da ABC sun daina yaɗa labarai daga ƙasar”.

Advertisement

Tun farko CNN ta sanar da dakatar da yaɗa labarai daga Rasha, sai kuma kafar labarai ta Bloomberg ta ce ma’aikatanta sun dakatar da aiki a ƙasar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *