Ma’aikatar cikin gidan Saudiyya ce ta sanar da ɗage dakatar da ibadar a ranar Lahadi kamar yadda shafin hukumomin da ke kula da Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina ya bayyana.
Wannan na zuwa bayan ɗage haramcin hanawa ƙasashe kusan 20 shiga ƙasar saboda annobar korona
Matakin ya shafi Najeriya da Saudiyya ta hana jiragen da suka fito daga ƙasar shiga ƙasarta saboda tsoron annobar korona.
Matakin kuma ya shafi ƙasashen Afghanistan da Afirka Ta Kudu da Namibia da Botswana da Zimbabwe da Lesotho da Eswatini da Mozambique da Malawi da Mauritius da Zambia da Madagascar da Angola da Seychelles da Comoros da kuma Ethiopia, kamar yadda shafin hukumomin da ke kula da Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina ya bayyana.
Yanzu dukkanin ƙasashe za su iya shiga Saudiyya domin aikin Umrah, yayin da azumi ya rage saura ƙasa da wata ɗaya, lokacin da galibi ake aikin Umrah.
Hukumomin Saudiyya sun kuma sanar da ɗage dukkanin matakai da aka ɗauka na ɗakile korona ciki har da bayar da tazara da sanya takunkumi a sarari.
Haka ma an kawo ƙarshen bayar da tazara a Masallatai biyu mafi daraja a Makkah da Madina, amma za a ci gaba da sanya takunkumi.
Yanzu baƙin da suka shiga Saudiyya ba sai sun killace kansu ba lokacin da suka isa.