Connect with us

News

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya sallami ma’aikata

Published

on

Daga Khadija Ibrahim Muhammad

 

 

 

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya sallami ma’aikata 513 na sashin wasanni na jihar kuma matakin ya fara aiki tun daga Litinin 21 ga watan Maris, 2022.

Sallamar aikin a cewar rahoton Vanguard, na cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ranar 4 ga watan Maris, 2022, kuma waɗan da lamarin ya shafa ya kunshi manya da ƙananan ma’aikata.

Advertisement

Gwamnatin ta bayyana cewa matakin wani bangare ne na kokarin da take na canza salon sashin wasanni zuwa hukumar wasanni ta jihar Edo.

Sanarwan ta ƙara da cewa gwamnati zata biya ma’aikatan da korar ta shafa hakkokinsu na albashin wata ɗaya.

Ma’aikatan da matakin sallamar ya shafa sun haɗa da, yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle, masu horarwa da kuma na ɓangaren shugabanci.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending