Connect with us

News

Yan Najeriya na Allah-wadai da dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci kan sukar Buhari

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Tun bayan da BBC Hausa da sauran kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito matakin dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci, kafofin sada zumunta na ƙasar suka cika da muhawara zazzafa da kuma Allah-wadai.

An dakatar da limamin daga Masallacin Apo da ke Abuja babban birnin ƙasar ne sakamakon huɗubarsa ta ranar Juma’a, inda a ciki ya soki Shugaba Buhari game da ƙin zuwa yi wa mutanen Kaduna jajen harin jirgin ƙasa da ya kashe mutum aƙalla takwas da kuma sace wasu da dama.

“Lokacin da yake neman ƙuri’a bai je Kaduna ba? To me ya sa ba zai je yi musu jaje ba?,” a cewar limamin.. “‘Yan siyasa sun gaza…musamman shugaban ƙasa…a ƙarƙashin mulkinka ‘yan fashi na saka wa ‘yan Najeriya haraji.”

Kwamatin masallacin ya ce sun dakatar da shi ne “saboda yana tunzura mutane” da kar su yi zaɓe bayan ya nemi ‘yan Najeriya da kar su fito zaɓe mai zuwa idan ba a kawo ƙarshen kashe-kashen da ‘yan bindiga ke aikatawa ba.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, sunan Sheikh Nuru Khalid ne ya fi komai tashe a dandalin Twitter na Najeriya, inda aka ambace shi sau fiye da 11,000. A Facebook ma, mutum kusan 10,000 ne ke tattaunawa a kan limamin.

Advertisement

Akasarin saƙonnin na ɗauke ne da bidiyon huɗubar da malamin ya yi cikin harsunan Hausa da Ingilishi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending