Connect with us

News

Hukumar Zabe Ta Baiwa Jam’iyyun Siyasa Shawarar Bin Ka’idoji Wajen Zaben Fidda Gwani

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

 

Advertisement

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa ta ba wa jam’iyu shawara a kan bin tsarin demokradiyyar cikin gida da dokokin zabe a wurin gudanar da zaben fidda gwani a yayin da ake tunkarar babban zaben 2023.

Hukumar ta ba da shawarar ne cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, jami’in wayar da kai na hukumar ya fitar a ranar Talata, a Abuja.

Advertisement

Okoye ya ce duk wata jam’iyya da ta gaza bin dokokin da aka tanada wurin gudanar da zaben fidda gwaninta ba za a amince da zabenta ba.

“Hukumar ta jaddadawa jam’iyun tsarin bin dokokin demokradiyyar cikin gida, kamar yanda yake tsare a kundin tsarin mulkin su,ka’idoji,dokar zabe da sauran tsare tsare da ka’idojin da hukumar ta bayar.

Advertisement

“Yan takarar su guda 1,491 na kananan hukumomi wanda za’a gudanar da zabensu a 2023, tilas ya fito daga mulkin dimokaradiyya, bayyananne da kuma ingantancen zaben fidda gwani, a kan tsarin da aka tanada a a sashe na 29 da 84 na kundin tsarin zabe na shekarar 2022.

“Duk jam’iyyar da ta gaza bin tanadin kundin tsarin zaben a wurin gudanar da zaben fidda gwanin ta, ba za a sa dan takarar ta a matsayin ta yake nema ba a babban zabe.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending