Sports
PSG ta fara yunkurin kulla yarjejeniya da Lukaku
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Dan wasan Chelsea Romelu Lukaku na shirin komawa Paris Saint-Germain a karshen kakar wasa ta bana, kamar yadda jaridar UK Sun ta ruwaito.
Rahotanni kuma sun ce tuni PSG ta fara tattaunawa da wakilan Lukaku kan kulla yejejeniya da shi.
PSG na iya bukatar sabon dan wasan gaba a karshen kakar wasa ta bana, a yayin da ake ta rade-radin cewa Kylian Mbappe na iya barin Paris Saint Germaine zuwa Real Madrid.
Wani akasi da aka samu a Chelsea dai shi ne, yadda Lukaku ya gaza taka leda kamar aka za ta, tun lokacin da ya koma Chelsea daga Inter Milan kan fan miliyan 98 a shekarar bara.
Dan wasan na Belgium ya ci kwallaye biyar ne kacal a kakar wasa ta bana.
Advertisements
