News
´BATANCI:ATIKU YACE BASHI YA WALLAFA SAKON SUKAR KASHE DALIBAR SOKOTO A SHAFINSA BA.
Daga Khadija Abdullahi Mahmud.
Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nisanta kansa daga wallafar Twitter wacce ya yi alawadai da kisan Deborah Samuel, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari
A jiya ne aka samu bayanai dangane da kisan dalibar, wacce kirista ce ‘yar aji biyu a kwalejin bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.
Sai dai bayan Atiku ya yi suka akan kisan nata, musulmai sun yi caa akansa su na cewa ba za su zabe shi ba, hakan ya sa ya dawo ya ce ba ya da masaniya akan wallafar
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.
Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.
Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:
“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”
Ya nesanta kansa daga wallafar ne bayan musulmai sun yi barazanar kin zabensa
Sai dai bayan wasu musulmai na arewa sun fara barazanar cewa ba za su zabe shi ba idan PDP ta tsayar da shi a matsayin dan takara, Atiku ya janye furucinsa.
Daga bisani Atiku ya goge wallafar da ya yi da kuma barazanar da aka dinga yi masa karkashin wallafar.
Sannan ya yi wata wallafa da harshen Hausa wacce ya nisanta kansa daga wallafar ta farko. Kuma a cewarsa duk wallafar da aka yi a shafukan sada zumuntarsa wacce ba ta zo da A. A. ba, ba shi ya rubuta ba.
“Da yamman nan na ga wata wallafa wacce aka yi ba da izininna ba. Ina amfani da wannan damar domin shaida wa kowa cewa duk wallafar da aka yi babu A. A. ba tawa ba ce. Ubangiji ya kare mu.”
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News6 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
