Connect with us

Sports

Sabbin tufafin Newcastle United mai kama da na ƴan wasan Saudiyya ya janyo suka

Published

on

Daga Usman Abdullahi jibirin

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Ingila, Newcastle United, ya ce ba shi da iko kan daya daga cikin tufafin da kungiyar ke son amfani da su a kakar mai kamawa – wanda da alama ya yi kama da irin na ƴan wasan Saudiyya.

Advertisement

Eddie Howe ya shaida wa manema labarai cewa yana sane da sukar tsarin tufafin.

Hotunan da aka fitar na samfurin tufafin ƙungiyar a kaka mai zuwa a makon da ya gabata ya janyo suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama.

Advertisement

Amnesty International ta ce bisa ga dukkan alamu wata hujja ce da ke nuna cewa gwamnatin Saudiyya na son yin amfani da Newcastle wajen kawar da kai daga ayyukanta na keta haƙƙin dan Adam.

A watan Oktoba ne wani kamfani da ke samun goyon bayan Masarautar Saudiyya ya karɓi ragamar Newcastle.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending