Politics
Gwamnonin APC sun samu saɓani kan zaɓin Buhari na ɗan takarar shugaban ƙasa
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rahotanni sun ce an kasa samun fahmtar juna tsakanin gwamnonin APC kan zaɓin da Buhari ya ba su na wanda yake son ya gaje shi.
Shaye-shayen miyagun kwayoyi ne ke ta’azzara rashin tsaro a Nijeriya — Ɗan Majalisa
Jaridar Premium Times ta ce gwamnonin na APC sun gana tsakaninsu bayan sun tattauna da shugaba Muhammadu Buhari kan batun wanda za a tsayar ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Gwamnonin sun gana ne, mintuna kaɗan bayan ganawar da suka yi da shugaba Buhari, a cewar jaridar.
Gwamnonin sun amince su sake zama da dare bayan kasa samun fahimtar juna a ganawar farko da suka yi.
Majiyar da jaridar ta zanta da ita daga cikin gwamnonin ta ce, bayan kansu ya rabu, wasu daga cikinsu sun bayar da shawarar a zaɓi biyu daga cikinsu ɗaya daga yankin arewa ɗaya daga kudu domin gabatarwa shugaban ƙasa.
Majiyar ta ce wasu gwamnonin arewa sun nuna cewa babu wani gwamna daga kudu da zai iya kada Atiku Abubakar ɗan takarar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, don haka ɗan arewa ne ya dace. Lamarin da ya fusata wasu gwamnonin Kudu.
A ganawar da suka yi da Buhari, shugaban ya shaidawa gwamnonin cewa zai so ya zaɓi wanda zai gaje shi kuma yana son gwamnoni su mara masa baya don yin hakan.
Shugaban ya kama hanyar zuwa Spain bayan ganawa da gwamnonin.
