Politics
Na so Peter Obi ya yi mun mataimakin shugaban kasa – Kwankwaso
Daga Maryam bashir musa
Tsohon gwamnan Kano da take takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ya so tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya yi masa mataimaki a takararsa ta shugaban kasa.
Sanata Kwankwaso ya ce lokacin da Peter Obi ya fice daga PDP ya so a ce ya shiga sabuwar jam’iyyar da ya kafa wato NNPP domin su yi takara tare.
Tsohon gwamnan da ke wadannan kalamai a tattaunawarsa da kafar Talabijin ta Channels a Najeriya, ya ce a mako mai zuwa za su gudanar da zaɓen fitar da gwani na takarar shugaban kasa, duk da cewa shi kaɗai ne ke takarar.
Babu inda nace zan kawo karshen tasirin Kwankwaso da Shekarau a siyasa — A A Zaura
Sai dai ya ce a yanzu NNPP za ta yi kokarin farautar wani fitacce daga Kudancin Najeriya domin su yi takara tare na neman tikitin shugaban kasa a zaɓen 2023.
