News
Yadda Za a Kawo Karshen Kallubalen Tsaro a Najeriya inji Buratai
Daga Sulaiman ado ahmad
Jakadar Najeriya a Jamhuriyar Benin, Laftanat Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya bayyana hanyoyin da za a bi don kawo karshen rashin tsaro, yana mai cewa kowa na da rawar da zai taka don kawo tsaro.
Gwamnatin Nijer Ta Dauki Sabbin Kwararrun Malaman Sakandare 2150
Buratai, tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasan Najeriya, ya yi magana a ranar Asabar a wani taron tsaro da aka yi na rana daya Arewa House a Abuja.
Ya ce a halin yanzu akwai kallubalen tsaro da dama a sassan kasar kamar ta’addanci a arewa maso gabas, yan bindiga da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, satar danyen mai da neman ballewa daga kasa a kudu maso kudu.
Buratai ya bada shawarar cewa dole a yi amfani da tsarin da kowanne dan kasa zai taka muhimmin rawa wurin magance kallubalen tsaro.
Ya yi bayanin cewa tsarin ya kunshi masu ruwa da tsaki daga cikin al’umma, kamar shugabannin addini, matasa, malamai, mata, kungiyoyin al’umma, kafafen watsa labarai, jami’an tsaro da tattara bayanan sirri. “Akwai bukatar a rika wayar da kan al’umma kan rawar da za su taka wurin samar da tsaro a kasar ta hanyar hukumomin kamar Ma’aikatan Wayar Da Kan Al’umma, NOA, da sauransu,” in ji shi.
Buratai ya kuma ce akwai bukatar a farfado da kamfanin kera makamai na DICON don magance kallubalen rashin isasun makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi.
Wannan na da muhimmanci domin cike gibin karancin makamai da sojojin Najeriya ke fama da shi da sabbin barazana.
“Don cimma hakan, Ma’aikatar Tsaro, tare da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki za su iya hada hannu don samar da kayan horaswa ga ma’aikatan DICON.
“Hakan zai kara kwarewarsu da makamai da za su kera wa sojojin Najeriya,” in ji shi.
Buratai ya kara da cewa garambawul da ake yi wa rundunar yan sandan Najeriya, siyo sabbin na’urorin tattara bayanan sirri da tsare iyakokin Najeriya zai taimaka sosai wurin samar da tsaro a kasar.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
