Connect with us

News

PDP ta kafa kwamitin nemo wa Atiku mataimaki

Published

on

Daga Maryam bashir musa 

 

 

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta kafa kwamitin da zai yi aikin nemo wa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, mataimaki.

Ba masu juya gwamnati ne ke sa ni daukar matakan siyasa ba – Buhari

 

Advertisement

Makonnin da suka wuce ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya lashe zaben fid da gwani, a matsayin wanda zai yi wa PDP takara a babban zaben 2023.

 

Shugaban jam’iyyar Sanata Iyorchia Ayu ne ya kaddamar da kwamitin a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ranar Talata.

 

Mataimakin Shugaban jam’iyyar shiyyar Arewaci Ambasada Umar Damagum ne zai jagoranci kwamitin, a daidai lokacin da hukumar zabe wato INEC ke dakon a mika mata sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da mataimaki a kwanaki masu zuwa.

 

Advertisement

Masu sharhin siyasa na ganin Atiku Abubakar, wanda ya fito daga Arewacin kasar, zai dauko mataimaki ne daga Kudanci, la’akari da yadda fasalin Najeriya yake.

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending