Connect with us

News

Yadda ɗaruruwan mutane ke rububin ɗiban ruwa a wata ƙatuwar rijiya a Indiya

Published

on

Khadija Abdullahi Mahmd.

 

 

 

Mutanen ƙauyen Khadimal a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya na cikin tsananin takurar rashin ruwa, inda suke sa rayuwarsu a haɗari kullum don samun ko da bokiti ɗaya ne na ruwa.

 

Advertisement

Ƙauyen, wanda yake yankin Amravati mai fama da matsanancin fari a gundumar Vidarbha, na yawan fama da tsananin zafi akai-akai.

ANA GAB DA FASALTA KUDIN TSARIN MULKIN LIBIYA

Mazauna yankin sun ce hukumomin ƙauyen kan aika tankar ruwa biyu ko uku kullum a juye a rijiyar, inda nan da nan sai mutane su fara rububin ɗiba don cika mazubansu.

 

Matsalar na ƙamari ne saboda rashin kyan ruwan da tsaftarsa – yara na yin rashin lafiya idan suka sha.

 

Advertisement

Bayan da sashen BBC Marathi ya wallafa wannan labaran Avishyant Panda – shugaban gundumar Amravati – ya ziyarci ƙauyen ya kuma ce gwamnatin za ta ƙara yawan ruwan da ake kai wa a tankokin.

 

Sannan ya ce za su yi ƙoƙarin shimfiɗa bututu don kawo ƙrshen matsalar ƙrancin ruwa a ƙauyen.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending