News
YAN SANDA DA YAN KATO DA GORA SUN KASHE MUTUM BIYU A KATSINA
Daga Yasir sani Abdullahi
Rundunar Yan sandan jahar KATSINA hadin giwwa da Yan Kato da gora sun dagele Wani hari da Yan ta,adda sukakai garin sabon dawa dake kauyen gundumar safana dake jahar KATSINA
Jaridar daily trust Hausa ta Gambo Isah, mai magana da yawun rundunar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a jiya Laraba a Katsina.
A cewarsa, lamarin ya afku ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuni da misalin karfe biyar na yamma, bayan da aka samu kiran gaggawa cewa ƴan ta’addar da yawansu ɗauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai hari kauyen.
“ Da samun rahoton, sai jami’an ‘yan sanda na yankin Safana su ka yi maza su ka mayar da martani bisa jagorancin Babban Jami’in ƴan sanda na safana inda ya ja tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga zuwa yankin.
“Daga nan sai suka yi artabu da ‘yan ta’addan da wata muguwar bindiga, inda suka kashe biyu daga cikinsu tare da dakile wannan mummunan aikin nasu,” inji shi.
Isah ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Idrisu Dabban ya yabawa ‘yan sanda, ‘yan kungiyar ƙato-da-gora da jama’ar yankin bisa jajircewarsu wajen kare al’umma daga hare-yan ta adda
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
