Connect with us

News

Yau Laraba Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance ministoci bakwai

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

A yau Laraba ake sa ran Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance sunayen ministoci bakwai waɗanda Shugaba Buhari ya miƙa sunayensu ga majalisar a makon da ya gabata.

Advertisement

Sigari na kashe sama da Ƴan Najeriya 30,000 a duk shekara – WHO

Shugaban Majalisar Dattawan Ahmad Lawan ne ya sanar da batun tantancewar a jiya Talata inda ya ce za a shafe zaman majalisar da za a yi yau domin tantance ministocin.

Advertisement

Cikin waɗanda za a tantance akwai Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano, Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Henry Ikechukwu Iko (Abia), Ademola Adegoroye (Ondo), Odum Odi (Rivers).

Sauran su ne Goodluck Nnana Opia (Imo) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi ).

Advertisement

A kwanakin baya ne dai wasu daga cikin ministocin Najeriya suka yi murabus saboda takarar da suka tsaya, lamarin da ya tilasta musu dole su yi murabus sakamakon sabuwar dokar zaɓe da ta tanadin haka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending