Connect with us

News

Gwamnatin Zamfara ta hana Sarakuna nadin Sarauta ba tare da amincewarta ba

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnan jihar Zamafara da ke arewa maso yammacin Najeriya Bello Matawalle, ya hana Sarakunan jihar nadin sarauta har sai sun samu amincewar gwamnatin jihar.

A wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan kafofin yada labari da sadarwa Zailani Bappa ya fitar, gwamnan ya ce ”Daga yanzu an umarci duk Sarakuna, da Hakimai, da Dagatai da ke jihar da su nemi amincewar gwamnatin jihar kafin su nada kowa, a kowanne mukami na Sarautar gargajiya”..

Advertisement

An dakatar da kamfanin jiragen sama na Dana Airlines daga aiki

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”umarnin ya zama wajibi ne domin kauce wa gurbata tsarin sarautar gargajiya, daga yanzu babu Sarki, ko Hakimi ,ko Dagacin da zai nada kowanne mukamin Sarauta, ba tare da samun amincewa da sahalewar gwamnatin jiha ba”.

Advertisement

”Bin wannan doka ya zama wajibi, domin kuwa gwamnati ta tanadi kwakkwaran mataki ga duk wanda ya saba wa dokar”, in ji sanarwar.

SOURCE BBC HAUSA

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending