Connect with us

News

Mutum 33 sun mutu bayan da motarsu ta fada cikin kogi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

Advertisement

Akalla mutum 33 ne suka mutu, wasu da yawa suka jikkata lokacin da wata mota makare da fasinjoji ta fada cikin kogin Nithi a kasar Kenya.

Hukumomin kasar sun an samu nasarar kubutar da mutum 10, a hatsarin da ya auku ranar Lahadi da daddare.

Advertisement

Matsalar Tsaro: NNPP Ta Bukaci Buhari Ya Yi Murabus

Motar dai na kan hanyarta ta zuwa birnin Mombasa daga garin Meru.

Advertisement

‘Yan sanda sun ce binciken farko da aka gudanar ya gano cewa burkin motar ne ya shanye lokacin da take tsaka da gudu.

Ana ci gaba da aikin ceto, yayin da ake tunanin adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa.

Advertisement

A ‘yan shekarun nan dai ana samun yawaitar hatsarin mota a titunan kasar Kenya.

BBC HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending