Connect with us

News

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta zabi sabon shugaba

Published

on

Rev. Daniel Okoh

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

An zabi Most Rev. Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN.

A wata sanarwa da Babban Sakataren kungiyar, Mista. Joseph Daramola, ya fitar a jiya Talata ne kungiyar ta sanar da samun sabon shugaban.

Dan Siyasa Ya Yi Karar Bokansa A EFCC Bayan Faduwa Zaben Neman Takara

Wannan ya kawo karshen wa’adin shugabancin Samson Olusupo Ayokunle tare da ‘yan majalisar zartarwa na kasa karkashin jagorancinsa.

Advertisement

An haifi sabon shugaban, wanda dan asalin jihar Ribas ne, a Kano ranar 12 ga watan Nuwamba na shekarar 1963.

Okoh wanda ya yi makarantar Dennis Memorial Grammar School, ta Onitsha, ya kammala jami’ar Patakwal a shekarar 1988, inda ya samu digiri a fannin kimiyyar siyasa da Ilimi.

A yau Laraba ne kungiyar za ta fara babban taronta inda a lokacin za ta gabatar da sabon shugabancin, wanda zai karbi ragamar gudanarwa ranar Juma’a 29 ga watan nan na Yuli 2022.

 

 

. NIGERIAN Trucker

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending