Kungiyoyin kare hakkin dan adam biyu sun shigar da ƙara a gaban kotun Paris kan Yarima Mohammed Bin Salman na Saudiyya, yayin da ya kai wata ziyara birnin Paris din da ke Faransa.
Shekara 7 na yi ina rubuta waƙar da nai wa Manzon Allah — Alan Waƙa
Takardar ƙarar da suka shigar mai dauke da shafi 42, na zargin Yariman da hannu a azabtarwa da ɓacewar Jamal Khashoggi, wanda daga baya wani jami’in Suadiyya ya hallaka a birnin Istabul a shekara ta 2018.
Takardar ƙorafin dai na cewa kisan Kashoggi wani shirye-shiryen abu ne.
Ganawar da Yarima Salman zai yi da Shugaba Macron na Faransa a wannan Alhamis din, wani ƙoƙari ne na sake farfaɗo da ƙimar a idon duniya.
