News
Kano: Ana Tsaka Da Samun Ruwan Sama Manoma Na Cigaba Da Kokawa Kan Tsadar Taki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Damina lokaci ne da ruwan sama yake sauka wanda hakan yake nuni da rani ya kawo karshe, inda al’ummomi daban-daban na duniya suke shuka nau’ikan abinda yafi tsira a yankin su.
Noma ya kasance wani ginshiki na rayuwar kowacce al’umma ta duniya birni da karkara, inda mutane da dama suke noma dan samun abin kaiwa bakin salati, wasu kuma ke yin sa don sayarwa a kasuwa.
Sai dai kuma a wannan lokaci da damina ta fara nisa ruwan sama ya ya waita, wasu manoman na ganin ruwan yana illa gawasu kayan amfanin gona duk da cewa ruwan bukatar sa ake ido rufe.
Kamar yadda wasu manoma suke hasashe anfi samun ruwan sama idan watan Agusta ya tsaya, amma a wannan lokacin ma iya cewa tun kafin watan Agusta ruwan ya fara yawa sosai, inda zaka ga an wuni ana ruwa wani lokacin ma har kwana ake yi anayi, duk da haka kuma marka-marka bata tsaya ba.
Bisa hakanne yasa JARIDAR ALKIBLAH ziyartar wasu manoma dake kauyuka don jin ya wannan yanayi yake shafar amfanin gonar da suke nomawa, inda taya da zango a kauyen Dalawa dake karamar Hukumar Albasu.
Kwankwaso Ya Gargadi ’Yan Majalisa Kan Tsige Buhari
Wani manomi mai suna Abdullahi da wakilinmu ya iske shi a gonar sa yana noma dai-dai lokacin da hadiri ya gangamo yana kokarin tafiya gida Inda ya bayyana cewa;
“Wasu kayan amfanin gona basa son ruwan sama yayi musu yawa kamar kankana da sauran dangin su, amma irin su Dawa, Maiwa, Gero Gyada, Wake, Dankali, Rogo, Masara, Shinkafa, duk suna bukatar ruwan sama musamman ma idan damina tazo karshe, a wannan lokacin idan ruwan sama bai ishe su ba komai na iya faruwa.”
“Ita Kankana bata son ruwa yayi mata yawa saboda idan ruwan ya yi mata yawa rubewa takeyi tafison ban iska, wato idan an samu ruwa yau akai kamar kwan biyu ba’a samu ruwa ba, hakan yana sanyawa tayi kyau a sameta” acewarsa.
Shi kuwa wani manomi mai suna Sale Yakub cewa ya yi;
“duk da wani lokacin ruwa yana yiwa amfanin gona yawa amma ahakan muna son sa domin lokacinsane wata rana ma sai mun bukaci ayi mana shi amma saboda ba lokacin yin sa bane baza’a yi shi ba.”
Ya kara da cewa “amfanin gonar da yafi son ruwa itace shinkafa domin ita idan ruwan sama yayi karanci bata yi sai kayi mata bar ruwa, idan da rijiya a wajen idan kuma babu sai ka zuba mata ido ta kone kanaji kana gani babu yadda ka iya”.
“Kamar dai shekarar data gabata da aka samu karancin ruwan sama a karshen damina, wanda hakan yasa manoma da yawa sunyi asarar shinkafar da suka noma, hakan ya shafi kokarin manoma na wadatar da kasar da shinkafar gida dan ciyar da al’ummar kasar nan”
“Saboda mu muna son ruwa lokacin sane kuma fatan mu Allah yasa daminar bana tayi harshe kada mu samu irin daminar shekarar data gabata domin manoma da dama sunyi asara.”
“Duk da haka a wannan shekarar a kokarin da manoma suke yi na ganin sun wadatar da kasar nan da shinkafa, kokarin nasu yana neman tashi abanza duba da irin tsadar da takin zamani yake yi a yanzu haka, a shekarar data gabata ana sayar da mudun takin yuriya akan naira 750 zuwa 800 inda a bana ake sayar da mudunsa akan naira 1,350 zuwa 1,400 wanda a yanzu buhun sa yakai Naira 23,800, sai takin
Dangote ana sayar da shi kan naira 1,350, wanda buhun sa yaka naira 21,000,sai NPK 20-10-10 ana sayar dashi kan naira 2200, kan kowanne mudu daya wanda buhun sa yakai Naira 26,400.
“Shima takin shugabn kasa Buhari wanda ake sayar da buhun sa farkon shigowar sa akan naira 5500, yanzu ana sayar da mudun sa kusan naira 1,700 wanda ake sayara da buhunsa ayanzu akan Naira 17,000,hakan yasa da yawa daga cikin manoman shinkafar komawa noman Dawa, Wake, Gero, Maiwa da sauransu”.
“Muna kiga gwamnati da ta duba halin da manoma suke ciki ta samar da takin mai sauki ga manoma wanda talakawa zasu iya saye”
Shima dai wani manomi Mustapha Yaura da wakilinmu ya tarar da shi a gwagwarandan dake karamar hukamar Albasu jihar Kano cewa yayi
“Ai shi ruwa rahama ne domin duk inda kaga ruwa to akwai albarka a wajen shiyasa ta bangarena ban damu da yawan sa ba nidai fatana Allah ya bamu dai-dai damu wanda bazai fi karfinmu yayi barna ba”
