Connect with us

News

Buhari ya gana da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ‘yan bindiga suka sako

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan da ‘yan bindiga suka sace daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris.

Advertisement

Shugaban kasar ya gana da mutanen ne ranar Alhamis a fadars Aso Villa da ke Abuja kwana daya bayan sako karin mutum biyar da aka sace a jirgin kasan.

Ko da yake kawo yanzu ba a bayyana batun da suka tattauna ba, amma hakan na faruwa ne makonni kadan bayan ‘yan bindigar sun sha alwashin sace shi kansa shugaban kasar da kuma gwamnan Jihar Kaduna Nasir Elrufai.

Advertisement

Sun yi barazanar sace shugaban kasar ne a wani bidiyo da suka fitar wanda ya nuna su suna lakada wa fasinjojin duka.

Buhari

A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne masu tayar da ƙayar baya suka kai wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari da daddare.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending