News
An tsare tsohuwar jakadar Burtaniya tare da mijinta a Myanmar
Daga Muslim yunus Abdullahi
Hukumomi a Myanmar, sun tsare tsohuwar jakadar Burtaniya a kasar tare da mijinta.
Ana zargin Vicky Bowman, da laifin take dokokin izinin shiga kasar, sannan ana zargin mijin da taimaka mata zama a kasar.
Ambaliyar ruwa ta shafi mutum miliyan 33 a Pakistan
Idan aka same su da laifi, za su fuskanci daurin shekara biyar a gidan kaso.
A shekarar 2002 ne Ms Bowman, ta je Myanmar a matsayin jakadar Birtaniya a kasar, ta kuma shafe shekaru hudu ta na aiki a can.
A yanzu ita ce shugabar kungiyar da ke wayar da kan ‘yan kasuwa a kan yadda za su tafiyar da harkokinsu a Myanmar ta hanyar bin doka da oda.
BBC News
Advertisements
