Ministar kula da yanayi a Pakistan ta ce fiye da mutane miliyan 33 ne ambaliyar ruwan da aka yi a kasar ta shafa.
Ministar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa,tun daga watan Yunin da ya wuce kawo yanzu fiye da mutane 900 ne suka rasa ransu sakamakon mamakon ruwan sama da kuma ambaliyar ruwan da ake ci gaba da samu a kasar.
An lakada wa ‘yan jarida duka a Zimbabwe
Ta ce gwamnatin kasar na nan na kokari wajen taimaka wa wadanda iftila’in ya shafa.
Kasar dai na bukatar karin tallafi daga kasashen duniya don agaza wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
Sherry Rehman, ta ce tun bayan saukar damunar bana ake fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar abin da ya jnyo ambaliyar ruwa a yankuna da dama na kasar.
Ta ce sama da gidaje 400 ne suka rushe, baya ga tursasawa mutane akalla dubu 184 barin muhallansu
BBC News
