Connect with us

News

Sufeto Janar Ya Gargaɗi ‘Yan Sanda Kada Su Goyi Bayan Wata Jam’iyya Lokacin Kamfen

Published

on

Police

 

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya umarci ɗaukacin ‘yan sandan Najeriya kada su tsaya a tsakiya ba tare da nuna goyon bayan su ga kowace jam’iyya ba a lokutan kamfen har zuwa kammala zaɓe.

Advertisement

Baba ya yi wannan gargaɗin a lokacin da ya ke jawabi a taron manyan jami’an ‘yan sanda masu muƙamin Kwamishina abin da ya yi sama.

An shirya taron a Abuja, ƙasa da kwanaki bakwai kafin a fara kamfen na zaɓen shugaban ƙasa, wanda za a yi ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.

Advertisement

Sannan kuma ya gargaɗe su cewa a kullum su riƙa kasancewa cikin shiri, tare da nuna ƙwarewa da sanin ya kamata, cikin nuna adalci a tsakanin jam’iyyun siyasa.

Ya ƙara tunatar da su cewa su sani fa aikin su shi ne kare masu jefa ƙuri’a daga masu aikata duk wasu laifuka, sannan kuma su yi aikin su ba tare da nuna bambanci ko don kai ko fifita wasu kan wasu ba.

Advertisement

“A matsayin mu na masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da an yi zaɓe cikin kwanciyar hankali babu tashin hankali, ku sani inganci da sahihancin zaɓen 2023 ya rataya ne a wuyan mu bisa ma’aunin irin ƙwarewa da bin ƙa’idojin da su ka wajaba mu bi, ba tare da yin katsalandan ba.

“Kada mu sake mu bayar da ƙofar da za’a riƙa tababa a kan rawar da mu ka taka. Mu kasance mun samar da kyakkyawan tsaro, zaman lafiya da kuma tabbatar da zaɓe cikin lumana, ta yadda mu ma za mu bayar da ta mu gudummawar wajen samun ingantacciyar dimokraɗiyya da dawwamammen tsaro a cikin ƙasa,” inji shi.

Advertisement

Ya umarci kowa ya yi nazarin Dokokin Zaɓe da kuma Sharuɗɗan Ayyukan Ɗan Sanda a Lokutan Zaɓe.

Daga nan ya kuma gargaɗe su kada su bari wata jam’iyya ko wasu ɗaiɗaikun ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen biyan buƙatar su.

Advertisement

Daga nan ya yi kira ga Kwamishinonin ‘Yan Sanda na Jihohi 36 su haɗa kai da Kwamishinonin Zaɓe na jihohin su da kuma shugabannin jam’iyyu a jiha, domin su shata ranakun da kowace jam’iyyar da ta shiga zaɓe za ta yi rangadi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending