Ana zargin wani dalibin firamare dan shekara goma da yunkurin kashe malamarsa da wasu takwarorinsa dalibai 12 a garin Njimbam na yammacin Kamaru.
Rahotanni na cewa, malamar ta aiki dalibin ne don ya sayo mata alewa, amma sai aka yi zargin cewa an zuba guba a ciki.
Kotun Najeriya ta ba da umarnin a kamo wani dan Burtaniya
Malamar dai ta karbi alewar, inda ta sha sannan ta raba wa karin daliban ajinta.
Jim kadan da shan alewar ne, sai malama da daliban suka fara kukan ciwon ciki, kafin daga bisani ajin ya rude.
Tuni dai aka garzaya da marasa lafiyan zuwa asibiti, kuma zuwa yanzu babu rahoto na mutuwar wani a cikin wadanda suka sha alewar
