Jam’iyyar All Progressive Congress mai mulkin Najeriya ta ce shugaban kasar ne za yanke hukunci kan lokacin da za a fara yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.
Mai magana da yawun kwamiti yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar Mr Festus Keyamo ne ya bayyana haka bayan kammala taron da shugabannin jam’iyyar suka gudanar tare da gwamnoni da kuma kwamitin yakin neman zaben, a jiya Laraba.
Jam’iyyar dai ta yi ta dage kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar, sanadiyyar rashin jituwa game da mutanen da ke cikin kwamitin yakin neman zaben.
Mr Keyamo dai ya ce kawunan ƴaƴan jam’iyyar a hade suke.
