Sports
Neymar ya ce bai da hannu a badakalar komawarsa Barca daga Santos
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dan wasan tawagar Brazil Neymar ya sanar da wata kotu a Sifaniya cewar bai da hannu wajen kulla yarjejeniyar komawarsa Barcelona daga Santos a 2013.
Dan kwallon da ke taka leda a Paris St Germain ya ce ya saka hannu kan kunshin kwantiragi kamar yadda mahaifinsa ya umarce shi.
FIFA 2022: Kizz Daniel zai cashe a ranar bude gasar cin kofin duniya na ƙwallon ƙafa
Ana tuhamar Neymar da wasu mutun takwas da aikata zamba da cin hanci – batun da suka musanta aikata ba daidai ba.
Wani kamfanin zuba jari DIS shi ne ya ke da mallakar kaso 40 cikin 100 na cinikin, amma sai ya tashi ba ko sisi, bayan makuden kudin cinikin kamar yadda aka sanar a duniya ya bambanta da wanda aka bayar.
Sauran da ake tuhuma sun hada da mahaifan Neymar da wakilan kungiyoyin biyu da tsoffin shugabannin Barcelona, Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell da tsohon shugaban Santos, Odilio Rodrigues.
DIS na son a daure Neymar shekara biyar, yayin da masu shigar da kara a Sifaniya ke fatan a garkame dan wasan Brazil shekara biyu da tarar yuro miliyan 10, suna kuma son a daure Rusell a kuma ci tarar Barcelona.
