News
Abubuwa 8 Da Suka Kamata Ku Sani Game Da Sauya Fasalin Takardun Kuɗi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A ranar Laraba ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya ba da sanarwar sake fasalin wasu daga cikin takardun naira a ƙasar nan.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Abuja a yayin wani taron manema labarai.
Mutumin da ya shafe shekaru 50 bai yi wanka ba ya rasu
INDARANKA ta tsakuro muku wasu abubuwa takwas da suka kamata ku sani game da sake fasalin takardun nairar da CBN zai yi.
- Gwamnan CBN ne ya sanar da sake fasalin takardun naira na N200, N500 da N1000.
- Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya amince CBN ya sake fasali, ya samar tare da rarraba sabbin takardun nairar na N200, N500 da N1000.
- Sabbin takardun kuɗin za su fara zuwa hannun jama’a daga ranar 15 ga Disamba, 2022.
- Tsaffin takardun naira N200, N500 da N1000 za su daina aiki daga ranar 31 ga Janairu, 2023.
- CBN ya umarci dukkan Bankunan Ajiyar Kuɗaɗe, DMBs, su dawo masa da tsaffin takardun kuɗin.
- CBN zai ba bankunan sabbin takardun kuɗin bisa tsarin wanda ya fara zuwa shi zai fara samu.
- Babban Bankin Najeriyar ya umarci bankuna su tabbatar cibiyoyin karɓar kuɗaɗensu suna buɗe daga Litinin zuwa Asabar don ba abokan ciniki damar dawo da tsaffin kuɗin.
- An dakatar da bankuna cajar kuɗi idan mutum ya yi ajiya.
Advertisements
