Connect with us

News

An tafka muhawara tsakanin masu takarar kujerar gwamna a Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Kungiyar likitoci ta NMA a Najeriya, ta shirya muhawara a karon farko kan harkokin kula da lafiya ga ‘yan takarar gwamnan jihar.

 

Advertisement

Kungiyar ta gayyaci ‘yan takarar gwamnan jihar Kano mutum takwas inda suka bayyana shirye -shiryen da za su yiwa fannin kula da lafiya a jihar Kano.

2023: Za mu haɗa kai da INEC don dakile sayen ƙuri’u – EFCC

‘Yan takarar sun tafka muhawarar kan batun inganta lafiya da kayan aiki da kara ma’aikata da kuma kyautata yanayin aikin likitoci da tsaftar muhalli da kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara.

 

‘Yan takara takwas ne kungiyar likitoci suka gayyata amma biyar ne suka samu halarta.

 

Advertisement

Akwai Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC da Salihu Tanko Yakasai na PRP da Injiniya Bashir Ishaq Bashir na Labour Party da Malam Ibrahim Khalil na ADC sai kuma Sha’aban Ibrahim Sharada na jam’iyyar ADP wanda mataimakin sa Malam Rabiu Bako ya wakilta

 

Kungiyar likitocin da suka shirya wannan muhawara sun ce ba wai burinsu su kure kowa ba, amma a fahimci matsalar fannin lafiya a jihar Kano don su shirya yadda za su gyara.

 

Sai dai ‘yan takarar jam’iyyar PDP da NNPP ba su halarci taron muhawarar ba.

 

Advertisement

Daga bayanan da BBC ta samu NNPP sun ce an basu goron gayyata a makare a dai-dai lokacin da dan takararsu ke halarta wani taro.

 

Su kuwa PDP uzuri suka bayar kasancewar mutumin da ke ikirarin shi ne dan takarar gwamna a Kano yana halartar wani taro.

 

Cibiyar kwararrun akantoci ta kasa ma, reshen jihar Kano sun ce za su shirya irin wannan muhawara ranar 8 zuwa 9 ga watan Disamba 2022.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending