Connect with us

News

Jami’an tsaro sun kai samame gidajen karuwai tare da kubutar da ‘yan mata 50

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

Advertisement

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta ce ta samu nasarar kubutar da ‘yan mata 50, wadanda ta yi zargin cewa an tilasta musu shiga karuwanci a wasu gidajen karuwai biyu a birnin Fatakwal da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Jaridar The Cable a Najeriya ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na sansanin sojin ruwa da ke jihar Richard Iginla, na bayyana cewa a yayin samamen sun kama mutum uku da suke zargi da safarar ‘yan matan -wadanda wasunsu shekarunsu ba su fi 14 ba – domin tilasta musu yin karuwanci.

Advertisement

Bom Ya Kashe Mutum 100 A Somaliya

Ya ce Sun kaddamar da samamen ne tare da hadin gwiwwar hukumar yaki da safarar bil-adama ta kasar wato (NAPTIP) da kuma rundunar tsaro da Civil Defence.

Advertisement

Ya ci gaba da cewa ”Mun samu bayanan sirri daga hukumar NAPTIP, wadda ta dade tana bibiyar gidajen karuwan da ake tilasta wa mata galibinsu ‘yan mata yin karuwanci. Daga nan sai muka shirya rundunar hadin gwiwwa cikin gaggawa muka kuma samu nasarar kubutar da wadannan mata”.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending