Connect with us

News

EFCC na binciken aikin wuta na Mambila, in ji minista

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Kwamitin lura da harkokin wuta na Majalisar Dattawan Najeriya ya bayyana aikin gina madatsar ruwa ta samar da wutar lantarki na Mambila a matsayin fata kawai duk da biliyoyin naira da aka kashewa aikin.

Advertisement

 

Ministan wutar lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu shi ne ya bayyana haka duk da dimbin kudin da ake ware wa aikin a kasafin kudi na shekaera-shekara da ya kai biliyoyin naira.

Advertisement

Satar N1.4bn A Banki: EFCC Ta Kama Dan Takarar Majalisar NNPP A Kogi

Jaridar DailyTrust ta ruwaito ministan na fadar hakan ne yayin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, ke gudanar da bincike kan aikin.

Advertisement

 

Batun ya taso ne yayin zaman kare kasafin kudi na 2023 ranar Talata tare da Ministan wutar lantarki da sauran hukumomi da ke karkashin ma’aikatar.

Advertisement

 

Shugaban kwamitin Sanata Gabriel Suswam (PDP, Benue), ya ce abin takaici ne duk da dimbin kudin da aka yi ta ware wa aikin wanda tun shekara 30 baya aka tsara shi, ba abin da aka yi a aikin.

Advertisement

 

Sanatan ya ce tun 2017, ake ware wa aikin na Mambila kudi amma ba abin da aka yi duk da matsin lambar da Majalisun Dokoki da kuma ‘yan Najeriya suke yi.

Advertisement

 

Aikin madatsar ruwan wanda zai samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050, idan aka kammala shi zai kasance mafi girma a Najeriya sannan kuma daya daga cikin mafiya girma a Afirka.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending