News
Mutum 412 ne suka mutu a hatsarin ababen hawa cikin wata 10 a Legas – FRSC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadura ta Najeriya ta ce mutum 412 ne suka mutu yayin da mutum 522 suka samu munanan raunuka a haɗuran ababen hawa da suka auku a hanyoyin Legas tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba.
Babban jami’in hukumar mai lura da shiyyar Legas Olusegun Ogungbemide -wanda ya wakilci babban shugaban hukumar – a taron ranar tunawa da waɗanda hatsarin kan tituna ya rutsa da su ne ya bayyana haka a birnin na Legas.
Za mu cire tallafin man fetur a 2023 – Gwamnatin tarayya
Ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa gudun wuce kima, da rashin gyaran ababen hawa, da tuƙin ganganci a matsayin abubuwan da suke haddasa aukuwar mafi yawan haduran da ake gamuwa da su.
Ya ci gaba da cewa sauya wa direbobi ɗabi’a game da waɗancan abubuwa da na da matuƙar muhimmanci, wajen rage aukuwar hasuran.
